Ziyarar bazatq zuwa ga matar data haifi yan hudu a jihar Kebbi
cikin shagulgullan ranar mata ta duniya da aka gudanar na shera ta 2022, uwar gidan gwamnan jahar Kebbi, HE Dr. Zainab Shinkafi -Bagudu ta aika sakon sanbarka ga wata mata mai suna Aisha Murtala hadi da tallafin kayan hidimar yara da suka hada da abinci,tufafi, gidan sauro,sabulunan wanka dana wanki harma da kudaden da zasu qara taimaka ma mai gidanta malam Murtala Garba ta bangaren kula da lafiyar mahaifiya da ‘yayanta.
Aisha Murtala yar shakara 28 ce wadda ta fito daga garin Kurin Marina ta yankin Arewa LG, wadda ta haifi ‘yan hudu maza biyu mata biyu ta hanyar CS a FMC BIrnin Kebbi, Aisha dai wannan shine karo na biyu bayan haifa ‘yaya biyar datayi a shekaru qalilan da suka gabata inga a cikin biyar Allah ya karbi biyu ya barta ukku a duniya.
Dr Ashiru Ladan ne likitan daya tarbi tawagar uwargidan gwammna Khadimatuddeen a FMC da suka hada da Honorable Zara’u Wali, team A da wakilan gidauniyar MCF.Dr Ashiru yayi godiya da miqa jinjina ga mai dakin gwamnan kan irin taimakawa al’umma da take gabatarwa ta kowane fanni ba tare da gajiyawa ba.