Labarai

Yadda wani matashi ya raunata mai shayi yakuma karbe masa Gas.

An tuhumin wani matashi da iakata laifin raunata Mai shatlyi da kuma karbe masa gasdin da yake sana’ar sa ta sai da shayi.

Wata babbar Kotun majistret mai lamba 70 da ke zamanta a Nomans Land, karkashin jagorancin mai shari’a Faruk Ibrahim Umar, Ta hora wani matashi mai suna Ibrahim Danlami Wanda yak zqune a Makafin Dala da ake zarginsa da sanadin raunata wani mai shayi da kuma kwace masa tukunyar Gas din sa ta siyar da shayin.

An bayyana cewar, matashin a ranar 26 ga watan 3, yayi amfani da wuka wajen ji wa matasa biyu rauni, a unguwar Gwammaja Inda daya daga cikin su mai shayi ne yay masa rauni a hannu wajen kokarin karbe masa gas din sa da kuma shadda da kudi naira Dubu 4.

Bayan an karantawa wannan matashi lefin sa ya karbi lefin Raunata mai shayi amma be karbi lefin kar bar masa shadda da kudi ba amma ya aminta da gas daya daukar masa.

Tuni mai Shari’a Alkhari Faruk Ibrahim Umar ya tasa keyarsa zuwa gidan kaso domin yaje yay wata 6 ba tare da biyan tara ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button