Labarai

ta cinna wuta a jikin ta bayan an hanata bikin zagowar Haihuwar ta.

Matar mai dauke da juna biyu ta aikata haka ne a Karamar Hukumar Uhuonmwode kusa da Benin a Jihar Edo.

Majiyarmu ta ce Ummi ta banka wa kanta wuta ne bayan ta wa kanta wanka da fetur, inda nan take ta kama da wuta.

Matar ba ta shekara da aure ba kamar yadda majiya mai tushe ta sanar
da Aminiya, inda ta ce a tsakiyar bara ce aka yi aurenta, kuma ta samu juna biyu.

Majiyar ta ci gaba da cewa, dalilin da ya sa ta aikata hakan shi ne, ta nemi mijinta ya bar ta ta tara kawayenta su yi shagalin bikin zagayowar ranar
aurenta sai mijin ya ki, inda ya ce mata, hakan ya saba wa Musulunci.

Majiyar ta ce hakan ne ya harzuka ta har ta kashe kanta.

Majiyar ta ce sai da ta jira mijin ya
fita wurin aiki, inda a cikin fushi ta dauki man fetur da suke zuba wa janareta ta bulbula wa jikinta ta kyasta ashana wuta ta kama, sai dai lokacin da ta fara konewa sai ta fara ihu, kuma ihun ne ya jawo hankalin makwabta suka kai
mata dauki, amma ta riga ta kone.

An kai ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar
Benin (UBTH), inda a can ne rai ya yi
halinsa.

Duk kokarin da wakilin Aminiya ya
yi don jin ta bakin iyayenta da mijinta
bai samu ba.

Kuma da ya tuntubi Babban Jami’in ’Yan sandan shiyyar da lamarin ya faru ya iske wayarsa a rufe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button