Advertising
Advertising
Labarai

Bidiyon Mutumin da yafi kowa tsufa a Duniya wanda har ake cewa Mutuwa ta manta da shi

Bidiyon Mutumin da yafi kowa tsufa a Duniya wanda har ake cewa Mutuwa ta manta da shi

Wani tsohon dan asalin kasar Japan mai suna Chitetsu Watanabe wanda aka bayyana shi a matsayin Mutumin da ya fi kowa yawan shekaru a duniya wanda ya mutu yana da shekatu 112.

Advertising

Jaridar Punch ta ruwaito a ranar 5 ga watan Maris na shekarar 1907 aka haifi Watanabe a kauyen Niigata dake Arewacin birnin Tokyo na kasar Japan, kuma ya mutu ne a ranar Lahadin da ta gabata a gidan kulawa da tsofaffi.

Duka duka tsakanin samun kambun kasancewa wanda yafi kowa tsufa a duniya da rasuwar sa bai wuce makonni biyu ba, kuma gidauniyar Guinness World Records ce ta bashi wannan kambu.

Watanabe yana da yara biyar, kuma ya bayyana sirrin tsawon rai da ya yi ga “Kada ka sake ka yi fushi ko a bata maka rai, kuma kada ka yawaita murmushi, Inji shi.

Advertising

Sai dai yace yana yawan shan askirim a yanzu haka mutumin da ya fi tsufa a Japan shi ne Issaku Tomoe dan shekara 110 kamar yadda kamfanin wallafa labarai ta Jiji ta tabbatar.

Sai dai babu tabbacin ko a duk duniya babu sa’ansa, haka zalika wanda ta fi tsufa a cikin mata ita ma ‘yar kasar Japan ce mai suna “Kane Tanaka” ‘yar shekara 117.

zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuga Mutumin da yafi kowa tsufa a Duniya wanda a yanzu haka ya rasu.

https://youtu.be/RcW8oMcqP0M

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button