Turkashi: Gwamman Barno Babagana Umar Zulum ya sauke duk Kwamishinonin sa
Farfesa Babagana Umara Zulum, Gwamnan jihar Borno ya amince da sauke dukkanin kwamishinonin jihar tasa ta Borno daga kan muƙaman su.
Saukewar wacce ta fara aiki nan take, na ƙunshe ne a cikin wata takarda wacce sakataren din-din-din na sha’anin mulki, Danjuma Ali, ya rattaɓawa hannu a madadin sakataren gwamnatin jihar, sannan aka rarrabawa ‘yan jarida a gidan gwamnatin jihar da ke a birnin Maiduguri.
A cikin takardar an umurci kwamishinonin da su miƙa ragamar ayyukan ofisoshin su a hannun sakatarorin din-din-din na ma’aikatun su.
Yadda Gwamnan ya fidda sanarwar dalilin sa na sauke su.
Takardar ta yi ƙarin bayanin cewa maƙasudin sauke kwamishinonin shine domin ba waɗanda ke da niyyar tsayawa takara a zaɓukan fidda gwani na jam’iyyar APC damar fitowa su tsaya ba tare da sun karya doka ba.
Idan zaa iya tunawa dai a cikin sabuwar dokar zaɓe da aka rattaɓawa hannu a kwanakin baya, an buƙaci masu rike da muƙaman siyasa da ke da burin tsayawa takara da su aje muƙaman su kafin lokacin zaɓe.