Mutanen gari sun hallaka wani dan bindiga bayan sun yi mummunar barna a harin da suka kai
Mutanen gari sun hallaka wani dan bindiga bayan sun yi mummunar barna a harin da suka kai
Daya daga cikin ‘yan bindigar da suka kai hari
Unguwar Bulus da Unguwar Gimbiya a Karamar Hukumar Chikun dake jihar Kaduna, ya yi gamo da karshensa a hannun mutanen gari.
A cewar jaridar Aminiya, rahotanni sun kuma
bayyana cewa, mutum uku daga yankunan
sun rasa rayukansu yayin harin da ’yan bindigar suka kai da misalin karfe 8 na daren ranar Alhamis.
Mazauna yankin sun bayyana cewa, maharan
sun shafe tsawon awanni suna harbe-harbe,
lamarin da ya sanya mutane da dama suka ranta ana kare.
Wani mazaunin yankin da aka kashe masa dan uwa a yayin harin ya ce, a halin yanzu suna cikin firgici da damuwa.
Ben Maigari ya ce, ‘yan bindigar sun kashe wani yaron dan uwansa sannan suka sace mahaifinsa a yayin harin da suka kai Unguwar Bulus.
Mun jiyo karar harbin bindiga tun kafin dare
ya raba don mutane da yawa ba su kwanta
ba, sai bayan komai ya lafa muka samu labarin
sun kashe yaron dan uwana sannan sun yi awon gaba da mahaifinsa.
Wasu mutum biyu ma sun rasa rayukansu amma jama’a sun kashe dan bindiga daya, a
cewar Ben, kazalika ya ce za’a birne matashin a ranar Juma’a a yankin.
Aminiya ta samu daga majiyar cewa, da bindigar da ya riga mu gidan gaskiya an harbe shine a goshi, ai dai Aminiya ta ce kokarin da wakilinta ya yi na jin ta bakin kakakin ‘yan sandan Jihar
Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya ci tura sakamakon rashin amsa wayarsa.