Advertising
Advertising
Labarai

Cin Amana: Zuciyata Kaman Zata fashe tunda naga mijina da budirwasa kiri kiri.

Ɗazu na dawo daga unguwa sai naga mijina ya ɗauko budurwarsa a mashin suna tafiya suna hira suna murmushi, tun daga nesa bai ganni ba, amma ni na ganshi.

Advertising

Sai da yazo gab da ni muka haɗa ido da shi yaga na haɗe rai, sai yazo gabana ya tsaya cikin sakin fuska da murmushi, sai cewa yayi sannu Auntynmu ina zakije ne haka kike faman sauri? Sai yace da budurwasa ki gaishe da ita matar ɗan uwana ce, ita kuma har tana gaishe da ni saboda bata san ni matarsa ba ce.

Tsabar baƙin ciki da takaici na rasa abinda zance, kawai nayi gaba na tafi na barsu a wajan shima yaja mashin ɗinsa suka tafi.

Yanzu na dawo gida ko abinci na kasa ci saboda baƙin ciki da takaicin abinda ya min, saboda cin fuska ba zai iya faɗawa budurwarsa ni matarsa ba ce saboda kada ranta ya ɓaci har da cewa ni Antynsa ce.

Advertising

Saboda haka nake neman shawararku, wanne irin mataki ya kamata na ɗauka idan ya dawo?

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button