Labaran Kannywood
Irin Tashin Hankalin da Jaruman Shirin Izzarso Suka Shiga Bayan Jin rasuwar Darakta Nura Mustapha Waye.
Jaruman cikin shirin izzar so sun shiga tashin hankali matuka tun bayan samun labarain rasuwar Daraktan shirin Nura Mustapha waye.
A safiyar yau asabar aka wayi gari da samun rasuwar Daraktan izzar so shiri mai dogon zango da ake Haskawa a tashar YouTube mai suna Bakori Tv.
Jarumi a cikin shirin shiya wallafa wannan rasuwar a shafin sa wanda da yawa mutane basu san da rasuwar ba in banda yasaka.
Da yawan yan harkar fim sun samu labarain rasuwar ne bazato sabida kusan mutane sunce lafiyar sa kalau dan haka sukaji rasuwar tasa bakatatan.