Advertising
Advertising
Labarai

Ina matuƙa son Buhari cewar Fasinjan da ya kuɓuta daga hannun ƴan ta’adda.

Hassan Usman, lauya kuma ɗaya daga cikin waɗanda harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya rutsa da su ya bayyana cewa shi har yanzu masoyin Buhari ne.

Advertising

Hassan na daga cikin fasinjoji hudu da aka sako daga hannun masu garkuwar a ranar 25 ga watan Yuli.

A wata hira da yake da ICIR, ya ce duk da cewa gwamnati mai ci ta gaza a fannin tsaro, amma har yanzu “ni ina matuƙar son Buhari .”

“Har yanzu ni masoyin Buhari ne , amma ta fuskar tsaro zan iya baiwa wannan gwamnati maki kaɗan Sabida ɗaya daga cikin babban nauyin da ke wuyansu shi ne ganin gwamnati ta tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin ƴan kasa,” inji shi. .

“Amma kamar yadda yake a yanzu, zan iya cewa gwamnati ta gaza sosai a fannin tsaro. Duk da ɗumbin kuɗaɗe da aka ware domin tsaro a Nijeriya, babu wani abu da ake gani a ƙasa”

Advertising
Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button