Advertising
Advertising
Labarai

Kungiya mai zaman kanta ta yiwa Karuwai gwaje-gwajen cututtuka kyauta a Onitsha HIV and AID

Wata Kungiya mai Zaman Kanta, NGO, mai suna Save Young Girls Motherhood Foundation, a jiya Talata ta gudanar da gwaje-gwajen cututtuka kyauta ga karuwai kyauta a Onitsha, Jihar Anambra.

Advertising

Gidauniyar ta fara gangamin wayar da kai a cikin Satumba 2021 don ceto ‘yan matan da suka tsinci kansu a cikin harkar jima’i na kudi.

Tawogar likitoci ce dai ta yi wa masu jima’i na kudin gwajin cutar hanta wato Hepatitis B da C, HIV da AIDS, Malaria, Typhoid, cututtukan 3 dake dauka ta jima’i , STIs, da dai sauransu a wajen taron.

Data ke zantawa da manema labarai a wajen
taron, Rev. Sister Dorathy Okoli, wacce ta kafa gidauniyar tace, da yawa daga cikin ‘yan matan sun koma yin lalata ne sabida tabarbarewar tattalin arziki talauci rashin kulawar iyaye da kuma tarbiyya.

Advertising

Na gamu da da yawa daga cikin wadannan
’yan matan kuma lokacin da suka bada labarin abubuwan da suka faru, na gane cewa suna shan wahala kuma suna bukatar taimako.

Da yawansu basu da matsuguni marayu iyayen su sun yi watsi da su wasu sun daina makaranta yayin da wasu kuma sun kammala karatunsu ba su da hanyar rayuwa, shine suka jefa kansu cikin sana’ar jima’i domin su rike kansu.

Suna bukatar taimako domin da yawa daga
cikinsu basa jin dadin abin da suke yi kuma
al’umma ba zasu iya cigaba da yin watsi da
wadannan ‘yan matan ba.

Wannan ne ya sa na fara wannan gidauniya domin ganin ko zamu iya kubutar da su daga
irin wannan rayuwa.

Suna bukatar tallafi kamar kiwon lafiya, abinci, matsuguni, gyarawa, ba da shawara da karfafawa, inji ta.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button