Advertising
Advertising
Labarai

Wannan shi ne karo na farko da na taba yin hadari A rayiwata: Dan wasan barkwanci, Sabinus (Bidiyo).

Fitaccen kuma Shahararren dan wasan barkwanci a Najeriya mai suna Sabinus AKA Mr Funny, Yayi wani jawabi cikin wani fai fan Bidiyon daya saki. A cikin Bidiyon yayi magana ne a game da Mumunan hadarin daya samu a yayin da yake tafiya a motar sa mai (Benz) Ya samu hadarin a Lahadi, 11 ga Satumba, 2022..

Advertising

Rahotanni sun bayyana cewa, dan wasan barkwanci yana tuki ne ajihar Legas, sai wani direban mota ya bugu masa mota, Ya kuma kutsa cikin motarsa.

Motar Sabinus, daga hotunan da aka dauka a wurin ta samu mummunar barna a gaban motar inda ta kai harin. Sai dai dan wasan barkwanci ya fito ba tare da jin rauni ba kuma yana cikin koshin lafiya kaman yadda ya bayyana a cikin wani faifan bidiyo.

Ya bayyana hakan ne a shafinsa na sada zumunta inda ya shawarci Al’umma da kada su rika shaye-shaye da tuki kuma a wani faifan bidiyo da ya yada shi ma, ya ga yana godiya ga Allah da ya ceci rayuwarsa.

Advertising

Haka zalika ya bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da ya taba yin hatsari kuma bai damu da hakan ba sabida daga Allah ne.

A karshe dan wasan yayi godiya ga masoyan sa da suka nuna damuwar su bayan sunji wannan mumunan hadarin.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button