Ya Kamata Abinda Ya Faru Da Ni Ya Zama Darasi Ga Kowannenmu Cewar Aminu Muhammad
Ya Kamata Abinda Ya Faru Da Ni Ya Zama Darasi Ga Kowannenmu Cewar Aminu Muhammad
ku karanta Sakon Aminu ga Aisha Buharí da kuma yan Nijeriya bayan an sako shi
Wannan Sakon ya fita ne a jiya bayan da matar Shugaban kasa ta yafewa Aminu Muhammad matashin daya gayawa matar shugaban kasa magana.
“Ina so na yi amfani da wannan dama, na bada hakuri ga dukkan wadanda na batawa rai, musamman mamarmu, Aisha Buhari. Ban yi niyyar na bata miki rai ba. Nagode da afuwarki, nagode Mama.
“Ina kuma so na yi amfani da wannan dama domin mika godiya ta ga wadanda suka taimaka min bayan na shiga mawuyacin hali, babu wanda ya isa ya tserewa Kaddarar Ubangiji, Amma ya Kamata abin da ya faru da ni ya zama darasi ga kowanenmu”
Ku cigaba da bibiyabr shafin mu dan samun zafafan labarai.