Labaran Kannywood

Dan takara shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yayi kyautar miliyan 50 ga yan Kannywood.

Dan takara shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yayi kyautar miliyan 50 ga yan Kannywood.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a zaben shekara 2023 Ya bawa Yan Kannywood Kyautar naira miliyan 50 a matsayin gudun mawa dan cigaban masana’antar tasu.

Dan takara shugaban kasar yabasu wannan kudi ne a yayin da suka hada wani zama a daren jiya lahadi a fadat gwamna Abdullahi Umar ganduje a jihar Kano.

Furodusa Abdul Amart cikin bayanin sa ya fadi manufar shirya wannan taron ya ce: Wannan taro na matasa ‘yan fim ne masu goyon bayan tafiyar Tinubu su ka shirya a ƙarƙashin Gidauniyar Kannywood domin su nuna irin ƙarfin goyon bayan da ya ke da shi a cikin ‘yan fim, Don haka su a shirye suke dan bashi duk wata gudunmawa data.

Shi ma a nasa jawabin, shugaban ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, ya bayyana Kannywood da wata babbar masana’antar da ta ke kawo kuɗin shiga da kuma samar da aikin yi ga matasa, don haka ya yi kira ga Tinubu da ya duba yadda masana’antar ta ke idan an kai ga nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button