Labaran Kannywood

Bidiyon Mawaki Musbahu M Ahmad ya maida martani ga Sheikh Dr Idris Abdulazeez Bauchi.

Jarumi kuma mawaki Musbahu M Ahmad ya saki wani bidiyo da yake maida martani zuwa ga Sheikh Dr Idris Abdulazeez Bauchi kan maganar daya fada akan yan Kannywood.

Malamin yayi wata magana ne a dai dai lokacin da yake tsaka da tsukar fina finan hausa na masana’antar kannywood, inda yake cewa.

”Ka gaya min ɗan fim ɗaya tak mai addini, in dai ɗan fim ɗin ne kirawo mana shi muyi masa tambayar menene addini.” Inji shi

Lamarin ya janyo cece kuce a shafukan sada zumunta inda wasu daga cikin masana’antar Kannywood ɗin suke yin martani akan waɗannan kalaman na Sheikh Dr Idris Abdulazeez Bauchi.

Daga cikin jaruman sun hada da Mawaki Musbahu M Ahmad kaman yadda yake fada cikin wani Bidiyo sa da zaku gani a kasan wannan rubutun.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button