Rahama Sadau Babu ruwan ku dani ku rabu dani nai rayiwata yadda nake so.
Turkashi fitacciyar jaruma a masana’antar kannywood Rahama Sadau ta maida martani ga masu damuwa da rayiwar ta.
Kaman yadda kowa ya sani jarumar Kannywood Rahama Sadau ta kasance mace ta farko a masana’antar wadda tafi kowa ce mace kawo ce-ce ku-ce a harkar Fim din Hausa.
Wanda wannan dalilin ne yasa yasa mutane kullum basu da zance sai nata a kafafen sada zumunta irin su facebook twitter da sauran su.
Wannan dalilin yasa jarumar tafidda wasu kalamai da take cewa “Ku bami in yi rayuwa ta yadda raina ke so tunda ba zaku iya cetona a ranar kiyama ba” Abinda jarumar ta fada haka yake saboda babu mai wuta da Aljanna sai Allah.
Kuma Ubangiji mai yawan gafara ne ga bayinsa, sannan ba’a yankewa mutum hukunci matukar yana a raye kuma ba’a shuga tsakanin bawa da Ubangiji.