Advertising
Advertising
Labarai

A karshe mawaki Davido ya goge faifan bidiyon nuna rashin da’a ga Musulunci bayan cece kucen da aka yi masa

A karshe mawaki Davido ya goge faifan bidiyon nuna rashin da'a ga Musulunci bayan cece kucen da aka yi masa

Mawaki David Adeleke da aka fi sani da Davido a karshe ya ji korafin jama’a tare da goge faifan bidiyon da ake ta cece-kuce a kai wanda aka dauka ana rawa a cikin Madallaci.

Advertising

Wannan na zuwa bayan mawakin ya wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna rashin mutunta addinin Musulunci da yaronsa Logos Olori ya hau, dake nuna rashin da’a ibadar Musulmai.

A ranar Asabar 22 ga watan Yuli Davido ya sha suka daga al’ummar Musulmai bayan wallafa faifan bidiyon da ke cin zarafin Musulunci a shafinsa na Twitter.

Musulmai da dama sun bayyana faifan bidiyon da cewa cin zarafi ne da kuma rashin mutunta addininsu inda aka gano matasa na sallah daga bisani suka koma rawa da waka.

Advertising

Sun zargi mawakin da rena addinin Musulunci inda yake hada sallah mai daraja da rawa da waka, Daily Trust ta tattaro.

Legit.ng Hausa ta tabbatar da goge faifan
bidiyon bayan ziyartar shafukan sada zumunta na mawakin,

Sun bukaci Davido da ya goge wakar tare da neman afuwa a wurin al’ummar Musulmi.

Daga cikin masu ta’ammali da kafar sadarwa da suka kushe bidiyon akwai jarumin Kannywood, Ali Nuhu da Bashir Ahmad, hadimin tsohon shugaban kasa Buhari.

A ranar Asabar 22 ga watan Yuli Davido ya sha suka daga al’ummar Musulmai bayan wallafa faifan bidiyon da ke cin zarafin Musulunci a shafinsa na Twitter.

Musulmai da dama sun bayyana faifan bidiyon da cewa cin zarafi ne da kuma rashin mutunta addininsu inda aka gano matasa na sallah daga bisani suka koma rawa da waka.

Sun zargi mawakin da rena addinin Musulunci inda ya ke hada sallah mai daraja da rawa da waka, Daily Trust ta tattaro.

Advertising
Back to top button