Labaran Kannywood
Bayyana bidiyon jaruma Rashida Abdullahi mai sa’a tana rawar banza ta janyowa kanta maganganu masara dadi

Tsohuwar Jarumar Masana’antar Kannywood rashida Abdullahi mai sa’a ta wallafa wata bidiyon ta sanye da wasu kananan kaya tana tikar rawa a shafin ta na sada zumunta, wanda hakan yayi sanadiyyar mutane suka yi ta mata cece-kuce.
Rashida ta bayyana a cikin bidiyon inda take tikar rawa bayan tasa wakar da aka yiwa tsohon sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Sanin kowa ne duk Jarumar data yi irin wannan abin dole ne mutane suyi mata maganganu kala-kala tare da cece-kuce, tun da wani lokacin abin da suke yana wuce gona da iri.
Domin ku kalli rawar da Rashida Abdullahi ma sa’a take wanda ta janyo mata cece-kuce, sai ku kalli bidiyon da muka saka ta a kasa.
Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.