Allah ya karbi rayuwar sa bayan ya sha artabu da ‘yan ta’addan Nageriya Allah yasa ya huta
Allah ya karbi rayuwar sa bayan ya sha artabu da 'yan ta'addan Nageriya Allah yasa ya huta
Marigayi DSP Abdullahi AbdulKadir Rano DPO
na garin Jibia a jihar Katsina wanda a yanzu Allah ya karbi rayuwar sa, naya da kokari wajan ganin an kawo karshen ‘yan ta’adda inda da yaji labarin to ba gudu ba ja da baya sai ya kokar ta a kai.
To a yanzu kuma shahahrarran marubucin nan Datti Assalafiy ya wallafa wani laabrin akan marigayin wato “DSP Abdullahi Abdulkadir”, kan irin kokarin da yake akan ‘yan ta’adda kafin Allah ya karbi rayuwar sa.
Inda Datti Assalafiy ya yi wallafa kamar haka.
Marigayi DSP Abdullahi AbdulKadir Rano DPO na garin Jibia a jihar Katsina yayi mutuwa irin na jarumai wadanda suke sadaukar da rayukansu a fagen yaki.
Da yaji labarin ‘yan ta’adda na zuwa ba gudu yayi ba, bai buya ba, kayan yaki ya dauka ya fita shi da yaransa ya jagorancesu domin ya kalubalanci barayin, ya shiryawa shahada domin ya kubutar da rayuwarsu wasu.
Matashin ‘dan sanda ne mai jini a jika, bai wuce shekaru 35 ba yaro ne yana cikin ganiyar jin dadinsa da iyalansa, amma ya hakura da wannan rayuwar ya sadaukar da ita wa Gwamnatin Nigeria.
Da wannan muke cewa ya kamata Gwamnatin Maigirma Shugaban kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya ta karrama DSP A.A Rano da lambar yabo na girmamawa, tare da karin girma domin iyalansa su amfana a taimakesu domin ya cancanci a masa hakan.
Muna rokon Allah Ya karbi shahadarsa, Allah
Ya kula masa da iyalansa.