Cikin wata bidiyo Fati Slow ta baiwa Sarkin waka hakuri kan cin mutuncin da ta masa bayan ya bata kudi
Tsohuwar jarumar masana’antar kannywood wacce tayi sharafin ta a shekatun baya wato Fati Usman wacce aka fi sanin ta da Fati Slow, ta wallafa wata bidiyo a shafin ta na sada zumunta instagram inda alamu suka nuna sun daidaita da Naziru M Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin waka.
Kamar yadda kuka sani Fati Slow ta wallafa wata bidiyo a shafin nata na sada zumunta inda take kalubalantar Sarkin waka kan wasu maganganu da ya jefi ‘yan kannywood da su, to sai ta bayyana a cikin bidiyon tana maida masa da martanin abin da ya fada.
Har ma take cewa, ya rantse da Allah kan cewa bai taba neman wata mace ba tun da yake, wanda rikin ya samo asali ne tun lokacin da BBC Hausa tayi shira da Ladin Cima wanda ita kuma a cikin shirar ta bayyana cewa , tun da fara harkar fim ba’a taba bata kudi sama da naira dubu biyar ba.
To a yau kuma a mun leka shafin Fati Slow inda mukaga ta wallafa wata bidiyo tare da Naziru Sarkin waka, inda take godiya ga Naziru Sarkun waka kan kyautar kudin da ya mata har naira Miliyan daya.
Sannan kuma ta tabbatar da cewar mawakin ya bata naira miliyan dayan da ya yi mata alkawari inda ta nemi yafiyarsa a kan cin mutuncin da tayi masa.
Wanda a cikin bidiyon aka ji Fati Slow tana fadin cewa.
Ga ni ga sarkin waka Naziru nagode Allah ya saka da alkhairi ya bani naira miliyan daya, dama harkac e ta kebura (talauci) kuma babu wanda bai san ta ba na nutsu yanzu.
Komai ya wuce sarki ka yi hakuri wallahi na yi maka hau, kuma ka ce ka yafe mun Alhamdulillahi wallahi nagode ma Allah, wannan ma arziki ce a rayuwa ta duniya.
Ga cikekkiyar bidiyon nan a kasa domin ku kalla.