Labaran Kannywood

Mansurah Isah ta ja kunnen masu tsokanar Fati Slow kan kudin da sarkin ya bata

Mansurah Isah taja kunnen masu tsokanar Fati Slow kan kudin da sarkin ya bata

Bayan Fati Slow ta amshe dunkulin kudin da Sarkin waka ya bata sai jama’a suka yi chaa a kan ta wasu na yaba mata da bata yi duhun kai ba ta amshe kudin, kuma ta bayyana cewa kebura ne suka sata har take wannan soki burutsin.

Inda wasu kuma suka sako ta a gaba da tsokana suna dauko tsofaffin bidiyoyin ta suka wallafa a madadin murnar wannan kudi da ta samu, da masu cewa ta tura musu nasu kason da dai sauran su.

Sai dai kawar ta tsohuwar jarumar kannywood Mansurah Isah ta gargadi masu tsokanar Fati Slow, inda ta wallafa hotunan ta wanda ta bayyana hakan kamar tunzura su take inda ta wallafa bidiyon Fati Slow a shafin ta ana mata karin ruwa gami da rubuta cewa.

Allah ya baki lafiya Fatima tana kan magani kuma tana samin sauki, sanarwa dan Allah ku daina amfani da bidiyon Fati kuna cin zarafin mutane, sabida kunsab tana neman taimako sannan da ‘yar karamar kyauta zata iya yin komai ta kasance mai biyayya a gare ka.

Abin da kuke yi kun san tunzurawa ne kuna tunzura ta kenan, sannan masu kiran ta kuna cewa ta baku kasan ku kusani kudin ya kare idan kuma kuna da magana kun san inda zaku same ni.

Ban ce zan rike fati ba amma zan yi iya bakin kokari na kafin na cigaba da tawa rayuwar.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji yadda bayanin yake ka wanda tashar “Tsakar Gida” ta wallafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button