Daki Auri Saurayi gara ki Auri Baban yaro.
DAGA Shuaibu Abdullahi
Jaridar Dimokuradiyya ta mallaki wani faifayin Bidiyo wanda ke bayyana wata matashiyar Budurwa tana baiwa Yan’uwan ta Yan mata Shawara kan cewa in dai suna son kwanciyar hankali da su Auri saurayi gwara su auri mai yawan shekaru Shuga Dady.
Matashiyar wacce bata bayyana sunan ta ba ta kafa hujja ne da wata ƙawarta data zabi wani kyakyawan saurayi kuma shi zata Aura.
Lokacin data ga Hoton saurayin ɗa kawarta ta zata Aura sai ta kira ta a waya take ce mata tayi ganganci ta yaya zata je ta Auri wanda ya fita kyau da haduwa tabbas ta hada kanta da rikici da hawan jini.
Tace babu yadda zaa yi taje ta Auri saurayi wanda ya fita kyau ba zai yiwu ba.
A saboda haka ne take baiwa Yan mata Yan’uwan ta shawara cewar indai mace tana bukatar kwanciyar hankali to ta auri mai yawan shekaru Shuga Dady, yanda babu wata mace da zata matsa mata.