Advertising
Advertising
Labarai

Wata yarinya mai shekara 16 ta rasu a rijiya a jihar Kano.

Wata yarinya me shekara 16 mai suna Hamida Bawale ta rasu bayan ta wada rijiya a Kofar Fada Gidan Sarki a karamar Hukumar Karaye da ke Jihar Kano.

Advertising

A jiya talata Kakakin Hukumar Kwana-kwana ta Kano Saminu Abdullahi ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a jiyan.

Sakinu yace lamarin ya faru da yammacin jiya Talata, bayan da Hukumar ta karbi kiran gaggawa da ga ofishin Hukumar Kare Farar-hula, NSCDC, reshen Karaye da misalin karfe 4:58.

A cewar Abdullahi, da ga karbar rahoton, sai hukumar ta yi maza ta tura jami’an ta na bangaren bada agaji, inda su ka isa wajen da misalin ƙarfe 5:04 na yamma.

Advertising

Da zuwan su, inji Abdullahi, sai su ka ɗauko Hamida, amma tuni rai ya yi halin sa, inda su ka miƙa gawar ta ta zuwa ga yayanta, Abdullahi Bawale.

Kakin ya kara da cewa marigayiyar ta gamu da ajalin ta ne bayan da ta je debo ruwa a rijiyar shine ta fada ciki.

Sai dai kuma sanarwar ta ce Hamida na fama da dan tabin hankali, Muna fatan Allah yaji kanta yay mata Rahama Ameen.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button