Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Mustapha Nabraska ya biyawa fursunonin 33 dake tsare a kotu tara domin suyi Azumin tare da Iyalan su

Ficaccan jarumin masana’antar kannywood Mustapha Badamasi wanda aka fi sani da Nabraska mun sami labarin cewa, ya biyawa fursunoni guda talatin da uku 33 tarar da aka yi musu a gidan yari domin su sami yin Azumin watan Ramadana tare da Iyalan su.

Advertising

An sako fursunonin guda talatin da uku 33 daga Gidan Yarin dake Gwauron Dutse a jihar Kano bayan Mustapha Nabraska ya biya tarar da ta sa aka tsare su a gidan yarin, sabida sun kasa biya tarar bayan kotu ta same su da laifukan da aka gurfanar da su a kai.

Mado Bala ya yabawa Mustapha Nabraska tare da yin alkari cewa, zai kasance mutum nagari, domin ya koyi babban darasi a tsare shin da aka yi a gidan yari.

Mustapha Nabraska ya bayyana cewa, ya yi hakan ne domin ya kara kwarin gwiwa ga wadanda ke da hali wajen faranta ran masu karamin karfi, musamman ganin cewa watan Azumin Ramadan ya kuranto.

Advertising

Unda ya kara da cewa, Gaskiya ba karamin tashin hankali bane ace mutum zai yi Azumi a gidan yari, shi ya sa naga dacewar a biya musu tarar da kotu ta yi musu da dan abin da zan iya.

Bayan haka ya kara da cewa, ya yi kira ga mawadata da kungiyoyi da kamfanonin dasu rika taimakawa wajen ceto rayuwar mutanen da ke cikin mawuyacin hali a gidajen yari, sabida sun kasa biyan bashi ko tarar da kotu ta yi musu kan wasu kananan laifuka.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button