Advertising
Advertising
Labarai

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi “NDLEA” ta kama Tramadol na kimanin Naira Biliyan 5 a jihohi 3

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi "NDLEA" ta kama Tramadol na kimanin Naira Biliyan 5 a jihohi 3

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun
Kwayoyi ta Kasa, NDLEA, ta kama kwayoyin
Tramadol da Exol 5 wajen guda miliyan 95 da kudin su ya kai kimanin Naira Biliyan 5 a jihohi uku.

Advertising

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da
Daraktan Yada Labarai da Wayar da kai na
NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a jiya Lahadi
a Abuja.

Babafemi ya bayyana cewa, an kama kwayoyin ne a film jirgin sama na Murtala Muhammed, MMIA, Legas, Abuja da kuma Jihar Edo.

Ya ce an gudanar da sunayen kama kayan ne
tare da hadin gwiwar Hukumar Kwastan ta
Kasa, NCS.

Advertising

Daga cikin adadin, a kwai kwali 214 na Tramadol 225 masu dauke da sunaye daban-daban har guda 10, wadanda su ka zama adadin 9, 219, 400 masu nauyin kilogiram 6, 384.5, wadanda kudinsu ya kai N4, 609, 700,000 a ranar Talata 29 ga Maris.

Wannan ya zone bayan kama kwali 85 na busasshen ganyen Khat mai nauyin kilo 1,327.35 da hukumar kwastan ta MMIA ta NDLEA ta yi a matsayin alamar hadin gwiwa
tsakanin hukumomin tsaro biyu.

A Abuja, an kama kimanin kwayoyi 228,740 da kafso-kafso na Tramadol da Exol 5 a ranar Juma’a, 1 ga Afrilu, a unguwar Abaji da ke babban birnin tarayya Abuja, an loda kayan ne a mota a Legas inda ta nufi Kano.

Ko da yake direban motar ya tsere cikin daji a lokacin da ake binciken motar, wasu mataimakansa biyu; Usman Abdulmumini mai shekaru 23 da Aminu Ahmad mai shekaru 22 an kama su, inji shi.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button