Advertising
Advertising
Labarai

Rashin Imani: Yadda wani matashi mai shekaru 18 ya kashe uwa da danta.

Wanda ake zargin ya haikewa matar ne a bakin kogi, inda taje domin yin wanka, tare da danta a gefen ta.

Advertising

“An ce, marigayiyar tayi kokarin yin turjiya ne ga kokarin da wanda ake zargin yayi domin yi mata fyade, amma cikin rashin sa’a sai ya rinjaye ta sakamakon ya fi karfin ta, inda ya danna ta a cikin ruwa har sai da ta mutu.

Hakan bai ishi mai laifin ba, sai ya kama dan nata, shima ya dilmiya shi a cikin ruwan har saida ya mutu.”

A sakamakon haka, an kama kama mai laifin, inda aka meka shi ofishin yan sanda na Lamurde, biyo bayan rahoton da mijin matar mai suna Alh. Usman Abdul, ya shigar, wanda shi a halin yanzu yake cikin tashin hankali, a sakamakon rashin matar sa da kuma dan sa. ” Kamar yadda rahoton ya nuna.

Advertising

Nguroje din ya ce, an umarci kwamashinan yan sanda, CP SK Akande, da ya gabatar da karin bincike akan lamarin, inda ya mika ragamar binciken ga mataimakin Kwamashinan wanda shine yake kula da bangaren SCID.

Haka kuma, ya yi kira ga al’umma da su kauracewa aikata laifuka, domin jami’an tsaro baza su yi kasa a gwiwa ba wajen zakulo masu laifi domin gurfanar da su domin su fuskanci hukuncin karya dokar kasa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button