Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Yadda Safara’u taja magana cikin wannan saban Bidiyon da tai Ranar Sallah.

Jaruma a cikin fina finan Hausa Safiya Yusuf wadda ake mata lakabi da Safara’u cikin Fim din da Arewa24 ke Haskawa kwana chasa’in.

Advertising

Safara’u ta ja magana cikin wani saban Bidiyo data saki wanda take rawa a harabar filin taro Ranar Sallah wanda Na wata sabuwar wakarta mai suna kwalelanka.

Mutane da dama sun dinga yi mata fatan shiriya tare da neman iyayenta ko kuma wasu da ke da iko da ita da su yi gaggawar dakatar da ita daga turbar da ta dauka.

Sai dai a jiya, ranar Laraba ta saki wasu bidiyoyinta da wata shiga ta kananun kaya tana rawa da waka bayan ta tara maza a wani wuri mai kama da shagalin sallah.

Advertising

A bidiyon ta hau wakar ta ta mai suna “Kwalelenka wacce mazan su ka dinga yi mata amshi tare da lika mata kudade.

Nan da nan mutane su ka tafi karkashin bidiyon su ka dinga yi mata fatan shiriya har da masu cewa ta zama abin tausayi don wannan hanyar da ta dauka ba mai kyau bace.

https://www.instagram.com/reel/CdJm9miIYYf/?igshid=YmMyMTA2M2Y=

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button