Advertising
Advertising
Labarai

A Gaugauta biyan diyar Matar nan mai juna biyu da kuma yaranta da mutun 6 cewar kungiyar Malamai da limaman Nigeriya.

Kungiyar Malamai da Limamai ta Najeriya ta umurci Gwamnatin jihar Anambara ta biya diyyar matar nan mai juna biyu da ya’yanta da sauran mutane 6 da aka k@she a jihar Anambara.

Advertising

Kazalika Kungiyar tayi Allah-wadai da wannan kis*an gilla kuma ta bukaci Gwamnatin Najeriya kada ta kuskura ta saki jagoran haramtacciyar Kungiyar IPOB Nnamdi Kanu saboda irin barnar da yan haramtacciyar Kungiyarsa ke aikatawa a yankin kudu.

Muryoyi ta ruwaito a cikin sanarwar da ta fitar a yau Alhamis Kungiyar ta kuma yi gargadi cewa an kaita bango don haka a yanzu zata zura ido taga irin matakin da Gwamnati tarayya da Gwamnatin jihar Anambara zata dauka akai, sannan tayi kashedin kada ta sake jin an zubda jinin wani musulmi a yankin kudu “saboda dokar kasa ta baiwa kowa damar zama yayi rayuwarsa a duk inda yake so”

Kuma muna kira Gwamnati ta kama Nnamdi Kanu da alhakin kis*an wannan mata da ya’yanta a sanya laifin kis@n nata a cikin jerin laifukan da ake tuhumarsa dashi a kotu kuma a bi mata hakkin ta.

Advertising

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button