Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Munfi Malaman Adini Fadakarwa cewar jarumi Ado Gwanja.

Mawakin da yai kaurin suna wajen wakar iskanci kuma jarumi a masana’antar shirya fina finan Hausa ta Kannywood Ado Isa Gwanja ya bayya cewa, sakonsu yana ishewa fiye da na Malamai.

Advertising

“Ana yarda da mu ana kallonmu, kuma ana sauraronmu fiye da yadda akewa Malamai, sabida a halin yanzu mutane sunfi karkata ga harkar nishadi fiye da jin wa’azi.”

“Saboda haka mafita kawai shine a daina kyamatar harkar fim, Malamai su shigo ciki domin a Musuluntar da harkar yadda za ta dace da addini da kuma al’adarmu.” Inji shi

Gwanja ya kara da cewar, haka Ilimin boko, Malamanmu na wancan lokaci da kuma mutanen kirki suka dinga kyamatarsa, aka bar harkar a matsayin kafirci, sai ya zamana mafi yawan wadanda suke Ilimin a wancan lokacin basu da llimin addini sai gashi a yanzu susuke mulkar al’umma.

Advertising

“Haka ma maganar ‘Film Village’ maimakon a bari a yi shi a Kano inyaso sai a shigo da Malamai da Hisbah cikin lamarin gudun kar a dinga wani abu da bai dace ba, amma sai aka hana gabaday, to idan aka yi shi a wata jihar makociyar Kano fa? Kaga abinda ake gudu dole shi zai faru, maimakon a yi shi a kano a Musuluntar da shi kaga aka yi shi a Kaduna baza a Musuluntar da shi ba, kuma dole zai shafi yan Kano.” Inji Gwanja.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button